Abinda Ya Sa Na Yi Aure Har Sau Bakwai – Jaruma Sadiya Kabala

0

Sadiya Kabala, jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, ta bayyana cewa ta yi aure har sau bakwai a cikin shirin fim din ‘kwadayi da buri’ domin nuna wa ‘yammata illolin da ke cikin kwadayi da son abin duniya.

Sadiya, wacce ta fito a matsayin ‘Salmah’ a cikin shirin fim din ta yi aure-aure barkatai sakamakon mu’amala da kawayen banza da suka rika ba ta guragun shawarwari.
Da ake tattauna wa da ita a kan rawar da ta taka a cikin shirin, jarumar ta ce ta fito da irin wannan hali ne domin ta nuna wa ‘yammata cewa shi fa kwadayi ba komai ba ne fa ce mabudin wahala.
Kazalika, ta kara da cewa darasin da shirin ke koyarwa shine da mai kudi da talaka, da samu da rashi duk daga Allah ne, kuma Allah zai iya bayar da arziki ga duk wanda ya ga dama, a kuma lokacin da ya ga dama, haka ma Allah zai iya talauta mai arziki idan ya ga dama.
A karshe, jarumar ta shawarci ‘yan uwanta ‘yammata da su kasance nagari, masu hakuri a duk yanayin da suka tsinci kansu a cikin rayuwar aure.
Wasu masu sharhin fina-finai sun bayyana cewa shirin fim din ‘kwadayi da buri’ ya yi daidai da dabi’ar ‘yammatan wannan zamani na son auren mazan da suke da arziki, ba tare da la’akari da halin mutum ko tsoron Allah ba.
Leave A Reply

Your email address will not be published.