An Sulhunta Ali Nuhu da Adam Zango
Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa an yi sulhu a tsakanin manyan fitattun jaruman nan na masana’antar shirya fina-finan Hausa, wato Ali Nuhu da Adam A. Zango a garin Kano, bayan gumurzun da suka tafka.
Sakataren kungiyar MOPPAN reshen jihar Kano, Malam Salisu Officer, ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ya na mai cewa, yanzu Ali zai janye karar da ya kai Adamu a kotu.