Ina da Sana ar Da Zan Dogara Da Kaina Ko Da Na Bar KannyWood – Adam Zango

0

Shahararren jarumin na dandalin shirya fina-finan Hausa kuma mawakin zamani, Adam A Zango ya bayyana cewa yana da sana’ar da zai iya dogaro da kansa ko da bayan ya bar sana’ar shirya fina-finai.

Jarumin ya bayyana hakan ne, a cikin wani zungureren rubutu da ya wallafa a shafukan sa na sada zumunta mai taken “Kannywood din yanzu ba kamar ta baya bace”.
Rubutun da ya yi tsokaci sosai akan irin yadda goyon bangarorin siyasa ke kokarin kawo cikasa a hadin kan ‘yan wasan Hausa.
Haka ma jarumin ya bada misalin yadda rashin hadin kai ya janyo rashin tallafawa wasu ‘yan wasa da suka tsinci kansu cikin yanayin jarabawar rayuwa.
A shafinsa na Instagram Adam Zango ya nuna alhini kan yadda a yanzu jaruman ke dar-dar wajen koda yin sharhi ne idan ya wallafa wani rubutu ko hoto a shafinsa don gudun kada fuskanci matsala a wajen ubannin gidansu.
Yace tun yanzu ma da yake raye kenan idan aka ce babu ransa wani hali iyalinsa za su tsinci kansu.
Source: @LegitHausa
Leave A Reply

Your email address will not be published.