Ali Nuhu da matarsa sun cika shekara 16 da aure

0

Fitaccen jarumin nan na Kannywood wanda ake yiwa lakabi da Sarki mai Kannywood mai sangaya, Ali Nuhu da Uwargidarsa Maimunatu sun cika shekaru 16 da aure.

Jarumin ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook inda ya nemi a taya su da addu’a da kuma fatan alkhairi kan Allah ya cci gaba da kara dankon soyayya a tsakaninsu.
Ma’auratan dai sun yi aure ne a watan Maris na shekarar 2003, sannan kuma Allah ya albarkace su da haihuwar yara biyu, mace daya, namiji daya wato Fatima da Ahmed.
Ga yadda jarumin ya rubuta a shafinsa na Facebook: “Alhamdulillah, yau mun cika shekaru 16. Muna godiya ga Allah SWT da ya nuna mana wannan ranar, sannan ya kara dankon soyayya tsakanin mu. Yan’uwa da abokan arziki a taya mu da addua.”

Wannan abun alfahari ne ga ma’auratan duba ga yadda ake fuskantar yawan mace-macen aure a tsakanin jaruman fim dama yankin Arewa baki daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.