Malam Shekarau Ya Bayyana A Fim Din ‘Al’ummarmu’ Don Hadin Kan Musulmi Da Kirista

0

Malam Shekarau Ya Bayyana A Fim Din ‘Al’ummarmu’ Don Hadin Kan Musulmi Da Kirista

Daga Nasir S. Gwangwazo

Sabon zababben sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon gwamnan jihar, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi wata fitowa ta musamman a farkon faifen bidiyon fim din ‘Al’ummarmu’ da karshensa, inda ya yi kira ga ma’abota kallon finafinan Hausa da su rungumi kallon finafinai irin Al’ummarmu, domin samar da hadin kai tsakanin Musulmi da Kirista.

Irin wannan bayyana a faifen finafinan Hausa ita ce irinta ta farko da a ka taba ganin wani fitaccen dan siyasa ya yi, domin karfafa gwiwar hadin kan kasa a Najeriya; kasar da ta ke da rinjayen mabiya addinan biyu, wato Musulmi da Kirista.

Shi dai wannan fim na Al’ummarmu an shirya shi ne da nufin kawo hadin kai tsakanin mabiya wadannan addinai, inda fitattun jarumai irin su Ibrahim Maishunku, Al’amin Buhari, Shehu Hassan Kano, Ladidi Tubeless, Ishaq Sidi Ishaq da sauransu su ka jagoranci wakilcin bangarorin biyu.

Bayanai sun nuna cewa, sakon da ke cikin fim din Al’ummarmu ne ya yi matukar birge zababben sanatan bayan da a ka nuna ma sa kafin ya fito kasuwa. Don haka ya amince a dauke shi da kyamara, saboda ya yi jan hankali da tunatarwa kan wannan sako mai matukar muhimmanci ga jama’ar kasar.

Amma rahotanni sun nuna cewa, Al’ummarmu ya sha tarnaki a hukumar tace finafinai ta jihar Kano a karkashin jagorancin Babban Sakatarenta, Isma’il Afakallahu, kafin ya samu sahalewar fita kasuwa, saboda sabanin da a ke zargin akwai tsakaninsa da masu shirin fim.

Majiyar mai tushe daga hukumar tace finafinai ta tabbar wa da wakilinmu cewa, da fari an saka wa fim din sunan ‘Arewa’ ne, saboda karfafi gwiwar hadin kai tsakanin Musulmi da Kiristan arewacin kasar, to amma shugaban hukumar ya dakile yin amfani da wannan suna, inda tilas ta sanya a ka sauya sunan fim din zuwa ‘Al’ummarmu’, duk da cewa a na ganin zai fi karbu wa da fa’ida da sunan ‘Arewa’ din.

Sai dai kodayake a yanzu haka fim din ya samu nasarar fitowa kasuwa bayan tsallake wadancan shingaye har a na ma sayar da shi a ko’ina a fadin kasar da makota, inda ya ke samun tagomashi.

Daga Jaridar LeadershiAyau

Leave A Reply

Your email address will not be published.