Kishin-kishin: Jaruma Nafisa Abdullahi ta kusa zama amarya
A cigaba da kawo maku labaran masana’antar shirya fina-finai ta Hausa wata Kanny wood, yau mun leko maku wani labari da ke ta yawo a masana’antar na cewa daya daga cikin fitattun fuskokin ta watau jaruma Nafisa Abdullahi na daf da zama amarya.
Wannan kishin-kishin din dai ta soma ne tun daga lokacin da jarumar ta je a shafin ta na dandalin sadarwar zamani na Tuwita ta rubata cewa “Yanzu ta tabbata” da turanci watau “It’s official” sannan kuma ta sa alamar zobe.