Ummi Zeezee Ta Bayyana Manyan Barayin Kannywood Su Biyar

0

Tauraruwar fina-finan Hausa, Ummi Zeezee ta yiwa wasu daga cikin abokan sana’arta kaca-kaca akan wasu kudi da tace dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar ya bayar a rabawa ‘yan Kannywood masu yinshi amma suka raba kudin tsakaninsu.

Abokan aikin nata da ta kira fitattun barayi 5 na Kannywood sune, Sani Musa Danja, Fati Muhammad, Zaharadeen Sani, Buhari Alamin da me bayar da umarni, Eemrana.
A cikin wani zungureren rubutu da tayi a shafinta na sada zumunta tace taso ta dauresu akan wannan abu amma mahaifiyarta ta hanata tace ta barsu da Allah.
Ga abinda tace kamar haka:
” Zuwa ga Fati Mohd, Sani Danja, Zaharaddeen Sani, Al’amin Buhari and director eemrana….
” A ranar JUMA’AR data gabata mai girma dan takaran shugaban kasa ta jam’iyar PDP Alhaji atiku Abubakar ya shirya wani taro da zaiyi da yan fim da kuma mawaka na kannywood dan gane da siyasarsa sai dai kuma Allah bai bashi ikon zuwa ba sai ya wakilta sir Bukola Saraki Wanda daya zo taron ya bada kyautan makudan kudi miliyoyi ga jarumai da kuma mawakan kannywood Wanda suke PDP suke kuma yiwa wazirin adamawa kamfen.
“Ammah sai gashi saboda son zuciya irin taku kuda na lissafo sunayenku kuka raba kudin a iya tsakaninku kawai ko wanne acikinku ya dau naira million hudu da rabi saboda zalinci tsantsa.
” To shi ai bukola sarakin ba ku kadai ya bawa kudin ba da zaku rabashi kawai a tsakanin ku shi cewa yayi ya bayar ga duk yan PDP na kannywood masu yin atiku wai ammah sai kuka fara kawo uzurin karya cewar wai acikinku ko wani mutum ya gaiyato mutum hamsin ne domin taron shiyasa kuka raba kudin a tsakaninku Wanda kuma karya ne ba wasu mutane hamsin hamsin da kuka kawo taron domin nima na je taron kuma a matsayina na babbar yar PDP mai manyan mukamai har biyu baku bani nawa kudin ba.
” Sai bayan an tashi daga taron ne na kira actor zaharaddeen sani awaya ina tambayar nawa kudin wai shine dan renin hankali ya aikomin da naira dubu 25k kawai sai kace ya daukeni yar jagaliyar siyasa koko ince ya daukeni matsiyaciya ko yar yunwa.
” Dan haka wannan wasika na muku ne domin in muku gargadi.
” Wallahi wallahi wallahi in aka sake hada taron daya shafi atiku abubakar kuka raba kudi bani aciki to duk sai na kulleku a DSS na abuja baza a barku ba har sai kun biyani kudina domin na tabbatar acikinku ba mai connection din da nake dashi a Nigeria kuma ko wannan kudin ma dakuka dannemin rabo na naso na rufeku duka shine danayiwa mamana waya na gayamata ta hanani tace rigima ba dadi in barku da Allah kawai zai sakamin shiyasa na rabu daku bawai dan ina tsoronku ba domin naga sauran mutanen da sukaje taron kuka hanasu hakkinsu tsoro ya hanasu magana.
” Dan haka acikinku in akwai dan iska to dan allah in an sake bada kyautan kudi akan siyasar atiku mutum yaci nawa yaga mezaifaru!macutan banza kawai!!”
Leave A Reply

Your email address will not be published.