Dole Jaruman KannyWood Su Nemi Wasu Hanyoyi Samun Kudi, Ba Sai Iya FIM Ba – Ali Nuhu

0
Dan wasan Kannywood, Ali Nuhu ya mayar da martani kan ikirarin da tsohon dan wasa Bashir Bala Ciroki ya yi na cewa Kannywood ta manta da shi .

Ya bayyana wa BBC cewa ‘yan wasa da yawa ba su da wani shiri ko tanadi da suke yi wa kansu, ganin cewa ba a dawwama a daukaka.

“Ita fa daukakarnan, wallahi dukkanmu da muke ciki bamu da tabbas a kanta”, a cewarsa.
Don haka, ya ce ko da masana’antar fim ba ta yi da dan wasa idan yana da wani shiri na neman kudi ba zai shiga halin kaka-ni-ka-yi ba.

Ya ce akwai ‘yan wasa da dama da suke sana’o’i don dogaro da kansu, kuma da za a shekara biyu ba a neme su wajen yin fim ba, ba za su fada halin wahala ba.

Sannan kuma, Ali Nuhu ya ce ya kamata ‘yan wasa su kyautata dangantakarsu da mutanen da suke hulda da su a lokacin da suke tashe.

‘Mun taso muna kallon wasan Ciroki’

Matashiya

Shafin sada zumunta na Instagram na Northern_hibiscuss ya bayyana abin da ya sa suka tara wa Bashir Bala Ciroki kudi fiye da naira 200,000 a ranar Talata.
An fara tara wa daya daga cikin `yan wasan farko da suka shahara a masana’antar fina-finan Hausa ne bayan da aka samu labarin cewa yana tallan kunun aya.
Aisha Falke, mai shafin Northern_herbiscuss ta ce sun tallafa wa dan wasan ne saboda tausayi.
A wata hira da gidan talabijin na Arewa24 , Ciroki ya yi ikirarin cewa masu shirya fina-finai da jaruman Kannywood sun daina sanya shi a fim, shi ya sa a yanzu yake sayar da kunun aya.

‘Ban taba tunanin ina da masoya a duniya irin wannan ba’

Shafin Northern_hibiscuss ya wallafa gangamin nema wa dan wasan taimako.
Tsallake Instagram wallafa daga northern_hibiscuss

Karshen Instagram wallafa daga northern_hibiscuss
Sai dai kafin hakan, jarumin fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya kalubalanci wani mai amfani da shafin Twitter cewa ya bayyana masa mutanen da abokin sana’arsa Ciroki, ya tallafa wa lokacin da tauraruwarsa ke haske a fagen wasan kwaikwayo.
Shi dai mutumin, wanda ke amfani da sunan Doctor Kiyawa, ya nuna rashin jin dadinsa ne kan yadda ya ce jaruman Kannywood sun yi watsi da Ciroki duk da cewa yana bukatar taimako.
Doctor Kiyawa ya yi zargin cewa mata kan shiga harkar fim cikin shekara guda su yi kudi amma mazan da suka kwashe shekara da shekaru suna harkar ba sa samun komai
“a Kannywood ne za ka ga mace ta shigo fim wannan shekarar amma ta fi wadda ya yi shekara 10 yana sana’ar fim kudi. Ali Nuhu, kai ne wadda yanzu jama’a suke gani da kima a Kannywood, don Allah ku yi wa [Chiroki] wani abu wanda shi ma ba zai manta cewa kun yi masa halacci ba.”
Sai dai a jerin martanin da Ali Nuhu ya yi wa masu irin wannan korafi, ya kalubalance su da su nuna masa irin taimakon da Cirokin ya bai wa Kannywood.
“Zan yi maka tambaya: lokacin da Ciroki yake tashe wa ya taimaka wa? Maimakon haka, a kan kudi mene ne ba ya yi wa masu shirya fim? Ya kamata mu san abin da muke yi.”
Ya ce bai kamata a rika yi wa ‘yan Kannywood rashin adalci ba, wajen dora alhakin gazawar wani daga cikinsu a kansu.
Jarumin ya ce babu wani da ke Kannywood da zai taimaka wa Ciroki, yana mai cewa “ya kamata ya dawo masana’antar ya sasanta da masu shirya fina-finai, sannan ya ci gaba da aiki kawai.”
Har ila yau Ciroki ya gode wa shafin Northern_hibiscuss dangane da tallafin naira 215, 000 da suka ba shi a Kano ranar Talata:
Tsallake Instagram wallafa 2 daga northern_hibiscuss

Karshen Instagram wallafa 2 daga northern_hibiscuss

BBCHausa.Com


Leave A Reply

Your email address will not be published.