Yadda siyasar Buhari da Atiku ya raba Kannywood gida biyu

0

Idan ba a manta ba farfajiyar Kannywood na daga cikin wadanda suka ba shugaban kasa Muhammadu Buhari gudunmawar gani kashe ni a zaben 2015.
‘Yan wasa da mawaka sun nuna fasaha da hazakar su wajen wasa gwanin su wato Shugaba Buhari da duk irin baiwar da mutum ya ke da shi a wancan lokaci.

A 2015, kusan duk wani da ya ke tunkaho a farfajiyar Kannywood, ya bada gudunmawar sa.
A siyasar 2019, Akalar ya karkata kadan domin da yawa cikin magoya bayan Buhari a wancan Karon sun kakkabe tabarmin su sannan sun goge takalman su sun dane jirgin tsohon shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Hassana Dalhat, fitacciya mai yin sharhi kan farfajiyar Fina-finai na Kannywood ta ce ko shakka babu akwai rabuwar kai da ya afko farfajiyar a bisa soyayyar dan takara.
” Idan kuka tuna a 2015, bayan Sani Danja da kowa ya sani yani tare da PDP, babu wani fitaccen dan wasa da ya nuna kan sa karara yana yi wa PDP aiki. Kusan dukkan su sun mara wa Buhari ne baya sannan suka tallata shi matuka ta hanyoyi da dama a yankin Arewacin Najeriya.

” Amma yanzu sai gashi dan takarar PDP wato Atiku Abubakar ya tsindumo farfajiyar da dankara-dankarar magoya baya sannan kuma fitattu suna yi masa aiki kamar yadda aka yi wa Buhari a 2015. Hakan ya nuna cewa akwai rabuwa na ra’ayi na siyasa a tsakanin su. Kamar yadda ake wake Buhari, haka ake wake Atiku sannan ana ci gaba da tallata shi a yankin na Arewa.
Bayan haka wani fitaccen dan wasa da ba ya so mu fadi sunan sa ya bayyana mana cewa, wannan baraka ya samo asaline ganin cewa wasu kan ware kan su suna nuna sune shafaffu da mai wajen nuna wa Buhari soyayya.

” Idan kuka duba, akwai wani ziyara da aka yi wa Buhari a dan kwanakin baya, wasu ne suka ware kan su suka zabi wadanda suke so su raka su suka tafi. Wasu da dama daga cikin wadanda suma sun bada gudunmawar su a nasara da aka samu a baya, watsi da su aka yi kacokan.
” Ire-iren haka duk suna daga cikin dalilan da ya sa wasu suka ga ay shima Atiku dan Arewa ne, musulmi zasu iya mara masa baya tunda abin ra’ayi ne na siyasa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.