Fina Finan KannyWood Da Zasuyi Tashe A Shekarar Nan 2019

0

Mun leka bangaren fina-finan Hausa na Kannywood inda mu ka kawo maku jerin fina-finan Hausa da za a saki a wannan shekarar da aka shiga ta 2019. Arewa Mobile ta zakulo wasu kadan daga cikin wadannan fina-finai.

Daga cikin manyan fim din da za a fitar a shekarar nan akwai:
1. SAREENA
Ali Nuhu da kuma Abubakar Bashir Mai Shadda ne su ke shirya wannan fim mai suna Sareena. Taurarin wannan fim din sun hada da Umar M. Sheridd, Abba El Mustapha da shi kan sa Ali Nuhu da kuma irin su Maryam Yahaya.
2. HAFEEZ
Daga cikin fim din da ake tunani za su yi tashe a bana akwai shirin Hafeez wanda shi ma Abubakar Mai Shadda ne yake shirya sa. Ali Nuhu ne babban Darektan wannan fim din mai dauke da Taurarin da ke cikin Sareena da wasun su.
3. SADAUKI
Wani fim kuma da aka kagara a fara kallo shi ne Sadauki wanda Hassan Giggs ya shirya kuma yake bada umarni. Taurarin fim din sun hada da Adam A Zango, Fati Washa, Fateema, Alhassan Kwalle da wasu manyan Taurarin Hausa.
Leave A Reply

Your email address will not be published.