Fim din Yaki A Soyayya ya shiga jerin manyan fina-finar 20 a Najeriya

0

Fim din Kannywood mai suna ‘Yaki A Soyayya’ ya shiga rukunin mayan fina-finan Najeriya 20
Yaki A Soyayya shine na 17 cikin fia-finai 20 da aka haska a sinima a fadin kasar daga ranar 28 ga watan Disamban 2018 zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2019
Furodusar fim din Nafisa Abdullahi tace tayi matukar farin ciki da fim dinta ya shiga jerin manyan fina-finai 20 a fadin Najeriya baki daya
Shahararren fim dinnan na Kannywood mai suna ‘Yaki A Soyayya’ ya shiga rukunin mayan fina-finan Najeriya 20.
Fim din ‘Yaki A Soyayya’ shine na 17 cikin fina-finai 20 da aka haska a sinima a fadin kasar daga ranar 28 ga watan Disamban 2018 zuwa ranar 3 ga watan Janairun 2019.
Kungiyar sinima na Najeriya wato Cinema Exhibitors Association of Nigeria (CEAN) ce ta saki jerin fina-finan a shafinta na twitter a ranar Laraba, 9 ga watan Janairu.
Kungiyar tayi bayanin cewa jerin fina-finan na daidai da bayanan yadda fina-finan suka yi fice a kullun a sinimomin Najeriya.
Daga jerin fina-finan, Yaki A Soyayya ta samu N722,000 a karshen mako sannan kimanin N1, 276, 000 a cikin kwanaki 7 kacal.
Da take martani, wacce ta shirya fim din Yaki A Soyayya, Nafisa Abdullahi tace tayi matukar farin ciki da fim dinta ya shiga jerin manyan fina-finai 20 a fadin Najeriya baki daya.
Leave A Reply

Your email address will not be published.