Watsamin Acid Da Akayi. Ya Zamomin Alkairi

0

Shahararren mawakin nan na fina-finan Hausa nan, Nura M Inuwa, yadda acid da aka watsa masa yayi masa amfani. Mawakin ya bayyana hakan ne a wata hira ta musamman da ya yi da BBC a kwanakin baya.
Nura ya ce abin da ya same shin ya kara masa son jama’a ne, maimakon gudun su.
Ga yadda cikakkiyar hirar ta kaya da shi.
“Ina yaro na fara da kuruciya, kawai sai na tsinci kaina ina waka a baya.Idan an bata min rai na kan yi waka, idan an faranta min rai hakan, na kan yi waka.”
Da aka tambaye shi akan mai ya dauki matsayin waka, Nura yace
“Na dauke ta a matsayin sana’a. Tana yi min amfani wajen tura sakonnin gyara ga al’umma. Fadakarwa da kuma nishadantarwa.”
Mu’azzam Idi Yari ne ya fara daura Nura M Inuwa akan hanyar waka.
“Sai ya rubuta wakar ya bani, salon kida, toh bayan ya bani nima da na karbe ta sai naje na ciccire wasu maganganu da nake ganin sun yi mun tsufa a cikin wakar, na gyara ta, nayi ta, ita ce wakar Salon Kida.”
“Na yarda Allah zai yi mun, kuma yayi mun. Shi ya cusa wa mutane kaunar wakokina a zukatansu suke son jin wakokina.”
Da aka tambaye shi kan yaushe aka watsa mashi wannan guba ta acid, sai ya kada baki yace: “A ranar Asabar ne, suka ce suna so su zo su koma Abuja, kuma shi wanda ya kira ni cewa matarsa, wadda zai aura ce ta dage sai Nura M Inuwa ya yi mata waka.
“Ni kuma kusan duk lokacin da aka yi mun irin wannan maganganun sai a karya min zuciyata. Wannan dalilin yasa suka kira ni, suka yaudare ni da sana’ata. Suka watsa min acid.”
“Wannan ya zama kusan tambari ko shaidar Nura M Inuwa, idan ka gan shi saida gilas, idan babu gilas to bashi bane.”
Leave A Reply

Your email address will not be published.