Nafisa Abdullahi Tayi Bayani Game Da Fadanta Da Hadiza Gabon

0

Fitacciyar jarumar Kannywood Nafisa Abdullahi ta ce a baya sun yi soyayya da Adam A. Zango, sai dai yanzu mutunci ne kawai tsakaninsu, amma ba soyayya ba.
A wata hira da ta yi da BBC Nafisa ta yi karin bayani game da matsayin Ali Nuhu a wajenta da kuma sauran abokan aikinta.
Nafisa Abdullahi na daga cikin jaruman da ke da farin jini sosai a fina-finan Kannywood
Jarumar wacce ta ce ta fito a fina-finai sama da 50, ta shaida wa BBC cewa fitattcen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya wuce matsayin aboki a wajenta.
“Ba zan kira Ali Nuhu aboki ba, ya wuce matsayin aboki.”
“Yadda zan zauna na yi magana da sauran jarumai, ba zan iya yi da Ali Nuhu ba,” in ji Nafisa.
Ta ce Ali Nuhu ne sanadin fara zuwanta Kannywwod.
Ta ce a Bauchi suka fara haduwa da Ali Nuhu a yayin da suke shirya wani fim na turanci, “A nan ne jarumin ya yi min alkawalin zai yi min fim din Sai wata rana.”
“Don haka ba za ka taba manta mafari ba”
Jarumar ta kuma ce ta fi yawan abokai maza fiye da mata.
Ta ce tana da abokai maza sosai a cikin al’umma, baya ga abokanta maza a Kannywood.

“Ban cika haduwa da Zango ba”

Nafisa Abdullahi

A shekarun baya an yi tunanin Nafisa Abdullahi da Adam Zango za su yi aure saboda yadda suka fito suka nuna suna matukar kaunar juna.
Amma Jarumar ta ce yanzu tsawon shekara biyar ba su tare. Ta ce kamar yadda Allah Ya hada su kuma Ya raba.
“Ba sai na fito na fara bayanin an yi kaza ko kaza ba, zama ne ya zo karshe muka rabu,” in ji Nafisa bayan an tambaye ta dalilin rabuwarsu.
“A baya mun fi ayyuka tare kuma an fi ganinmu tare amma yanzu ba mu cika haduwa da juna ba sosai saboda ban cika fitowa a fina-finai ba.”
Jarumar ta ce yanzu ta dauki Adam Zango a matsayin abokin aiki amma ba soyayya tsakaninsu.
Ta ce ba su cika haduwa da shi ba a yanzu. “Ba mu da wata matsala ta rashin jituwa da juna tsakani na da shi.”

Babbar kawar Nafisa

Nafisa Abdullahi da Halima AteteHakkin mallakar hoto@HALEEMAATETE

Jarumar ta ce dole a kowace irin haraka musamman a masana’anta akwai wanda taku ta zo daya.
Nafisa ta shaida wa BBC cewa jaruma Halima Atete ce babbar kawarta.
“Ta mu ta fi zuwa dadai da Halima Atete,” in ji ta.
Ta kara da cewa, Atete ce kadai ta yadda da ita da take iya bayyanawa sirrinta

Shin Nafisa ta shirya da Hadiza Gabon?

An dade dai Nafisa na gaba da jaruma Hadiza Gabon.
Kuma duk da ba ta amsa tambaya game da dalilin da ya janyo sabani tsakaninsu ba, amma ta ce abu ne da ya faru kusan shekara daya da rabi, kuma ya riga ya wuce.
“Ba ni son sake dauko wannan zancen.”
A shekarar 2017 ne fitattun jaruman guda biyu suka yi fada inda wasu rahotanni suka ce har da duka yayin da suke tsakar shirya wani fim.
Nafisa ta ce babu wata dangantaka tsakaninta da Hadiza Gabon, bayan an tambaye ta ko suna kiran juna a waya.
“Ba mu cika haduwa da Hadiza Gabon ba, idan mun hadu muna dan gaisawa.”

Shin Nafisa ba ta karin gashi?

Nafisa AbdullahiHakkin mallakar hoto@NAFEESAT_OFFICIAL

An tambayi Nafisa cewa shin ko tana karin gashi ne? ganin yadda take zuba hotuna a shafinta na Instagram gashi kwance a bayanta.
“Idan aka ga gashi nawa ne.”
“Idan gashi ya kwanta na Nafisa Abdullahi ne,” in ji jarumar.
Cc BBCHausa.Com
Leave A Reply

Your email address will not be published.