Maryam Booth Ta Musanta Batun Auren Sadiq Zazzabi

0
 

A ranar 30 ga watan jiya ne jarumar Kannywood, Maryam Booth ya wallafa wasu hotuna a shafinta na Instagram tare da mawaki Sadiq Zazzabi da suka yi kama da na kafin aure.
Hotunan dai sun haifar da cece-kuce bayan da aka yi ta yadawa cewa jarumar da mawakin sun kusa yin aure.
An yi ta yada hutunan a shafukan sada zumunta da cewar jarumar za ta yi aure, inda har wasu mabiyanta sun fara kiranta amarya.

Toh sai dai kamar yadda sakon da ke kan hotunan ya nuna, hotunan na wani fim ne mai Suna Gidan Biki da Booth da Zazzabi suka fito a ciki.
Booth ta tabbatar da wannan batu da kafar yada labarai ta BBC ta tuntube ta.
A cewarta “Ban yi aure ba, a wani fim ne da ake kan shirya wa,”.
Leave A Reply

Your email address will not be published.