Wasu Masoya Sun Fusata Adam A Zango Akan Siyasa
Shahararren mawaki kuma jaruma a fina-finan Hausa na Kannywood Adamu Abdullahi wanda aka fi sani da Adam A Zango ya bayyana cewa ba laifi bane don ya taya alhaji Atiku Abubakar murnar lashe zaben cikin gida na jam’iyar PDP da yayi.