Saurayi ya kashe kansa bayan budurwa ta ki amincewa da bukatar shi

0

A bun nema bai samu ba yayin da wani saurayi mai shekaru 29 ya kashe kansa ta hanyar rataya bayan ya nemi yayi kaura da budurwar shi.

An gano gawar shi tana lilo saman bishiya a yankin Shupikal dake nan garin Mutawatawa a kasar Zimbabwe.

Rundunar yan sanda na shiyar sun tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya faru a ranar 4 ga watan Agusta.
Rahotanni sun nuna cewa saurayin ya ziyarci gidan budurwar tasa ne inda ya bukace ta da su kaurace zuwa wani gari sabanin kin amicewar budurwar ya dauki matakin rataya kanshi.
Majiya sun shaida cewa budurwar taki amince ma bukatar da saurayin ya nama daga gare ta domin iyayen ta basu amince da soyayyar su.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda na shiyyar Tendai Mwanza yace jami’ai na cigaba da bincike kan lamarin. Yayi kira ga al’umma da su tabbatar sun warware duk wata sabani da suka samu ta hanyar da ya dace. Ya nuna takaicin sa bisa rasa ran da aka rasa sakamakon rashin daidaituwar kai.
Leave A Reply

Your email address will not be published.