Rahama Sadau Ta Caccaki Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar

0
Shahararriyar jaruma Kannywood da aka dakatar a dandalin shirya fina-finan Hausa wacce ta ke fice yanzu a Nollywood Rahma Sadau ta caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Wannan caccakar ya biyo bayan martanin da Atiku ya mayarwa da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan cewa matasan Nijeriya ba malalata bane.
Jarumar ta zargi Atiku da cewa sune umul abaisin lalacewar matasan kasar musamman a yankunan Arewa. Cewa su suka maida matasa yan daba.
Ta kuma jadadda cewa sun kwana da sanin cewa Buhari masoyin matasan kasar ne.
Rahma Sadau ta aikewa da Atiku Martani kamar haka. “Wai kana alfahari da matasa alhalin kune silar lalacewar matasan Nijeriya musamman yankinmu na Arewa a lokacin mulkinku na PDP da kuka mayar da matasa yan daba kuna amfani dasu a matsayin karnukan farauta suna yin ta’addanci kala kala dan ku samu mulki ko ta wani hali.
“Mu mun san Buhari masoyin matasan Nigeria ne dan haka matasa kada ku yadda wani dan jari hujja ya yaudareku. 2019 sai Baba insha Allah” Inji Rahama Sadau.
Rahma Sadau ta caccaki Atiku Abubakar https://t.co/fQ9PIkDLm2 pic.twitter.com/Xj7UIR4fHf

— NAIJ.com Hausa (@naijcomhausa) April 24, 2018

Leave A Reply

Your email address will not be published.