Kanu ya bayyana dalilin ziyarar sa ga Sheikh Pantami, kalli hotunan ganawar su

0

A Ranar, Laraba, tsohon dan wasan kwallon kafar Najeriya, Kanu Nwankwo, ya ziyarci Sheikh Isa Ali Pantami.

Kanu ya ziyarci Sheikh Pantami ne a ofishin hukumar bunkasa fasahar zamani(NITDA), wacce yake jagoranta, a birnin tarayya, Abuja.

Da yake bayyana dalilin ziyarar sa, Kanu, ya ce ya zabi ya ziyarci hukumar ne saboda kaf cikin hukumomin Najeriya babu wacce take burge shi kuma take taka rawar gani kamar hukumar NITDA.

A kwanakin baya ne dai rahotanni suka bayyana cewar, tsohon dan wasan kwallon kafar, Kanu, zai fito takarar neman shugabancin kasa.

Saidai daga bisani Kanu ya fito ya nesanta kansa daga wannan rahoto.

Kanu ya yi fice wajen aiyukan taimako da tallafawa masu karamin karfi, domin har wani asibiti ya gina domin duba masu matsalar ciwon zuciya kyauta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.