KISHIYA: Hauwa’u ta daba wa mijin ta kwalba a Zuciya daga cewa zai kara aure

0

Wata matan aure mai suna Hauwa’u ta daba wa mijin ta fasasshen kwalba a tsakiyar zuciyar sa saboda ya to mata barazanar yi mata kishiya.
Shekaran Hauwa da Bilyaminu 8 a aure amma babu da, shine yayi mata tayin kara mata, ashe ya kira wa kan sa ruwa ne.
Mai gidan Hauwa, Bilyaminu, yana nan kwance a asibitin Yariman Bakura dake Gusau.
Jami’in hulda da jama’a na asibitin Awwal Usman ya tabbatar da aukuwar wannan abu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Muhammad Shehu ya ce tuni an kama Hauwa tana tsare a ofishin ‘yan sanda ana ci gaba da bincike akai.
Leave A Reply

Your email address will not be published.