Duk ranar Talata da Laraba sai mahaifina ya kwana dani – Wata ‘yar shekara 12

0
Wata yarinya ‘yar shekara 12 ta sanar wa kotu a jihar Legas cewa mahaifinta mai suna Idoko yakan tilasta mata ya kwana da ita duk ranar Talata da Laraba a gidan su.
Jami’an tsaro sun gurfanar da mahaifin yarinyar ne a Kotu, ana tuhumar sa da tilasta wa ‘yarsa aikata alfasha kamar haka, wanda ya sabawa dokar kare hakkin dan yara kanana na kasa.
Shekara uku Kenan da Idoko ya saki mahaifiyar wannan yarinya sannan ya hana ta tafiya da yar a lokacin tana shekara 9 da haihuwa. Daga nan fa ya fara da yi mata fyade har ya kai ga sun saba duk Talata da Laraba za a buga harka.
Koto ta daga sauraron karar zuwa 12 ga watan Disamba, sannan an bada belin Idoko kan naira 200,000.
Leave A Reply

Your email address will not be published.