Wani Magidanci Ya Kashe Matar Sa Dake Da Cikin Wata 8 A Abuja

0
Wani magidanci Doosur Ankyoor mai shekaru 37 ya kashe matar sa dake dauke da cikin wata 8 da duka.
Yayin da ake sauraron karan a babbar kotun karan dake Abuja, lauyan da ya shigar da karan Donatus Abah ya fada wa kotun cewa Doosur ya aikata haka ne ranar 5 ga watan Yuni a gidan su dake kauyen Lugbe, Abuja.
Abah y ace haka kawai Doosur ya kama matarsa da mummunar duka wanda hakan ya kawo ajalinta da dan dake cikinta.
Duk da hakan lauyan da ke kare Doosur, Ocheme Adama ya nemi kotu ta bada belin sa domin ya sami damar kula da ya’yan su uku da ta bari.
Alkalin kotun Peter Affen ya yanke hukuncin daure Doosur a kurkukun Kuje sannan ya daga sauraron karan zuwa ranar 16 ga watan Nuwamba domin ci gaba da shari’ar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.