Karanta Labarin Matar Data Aure MazaJe Sha Takwas (18) Cikin Shekaru Shida

0

Wata yar 25 ta bayyana yadda ta auri mazaje 18 cikin shekara 6 da kuma yadda auren suka mutu

Wata mata mai shekaru 25, Martha Korchioga, ta girgiza masu bauta a lokacin da ake warkarwa da yin addu’o’in wata a cocin St. Luke’s African Church dake Gyenwase a karamar hukumar Ukum na Jihar Binuwai lokacin da ta yi ikirarin auren maza 18 a cikin shekara shida .
A rahoton Daily post, Korchioga wanda take yar karamar hukumar inda cocin yake ta bayyana haka yayin da je neman waraka daga cocin.
Tace duk namijin da ta hadu da shi sai ya neme ta da aure kuma yawanci auren baya wuce yan satutuka.
Duk namijin da ya hadu dani sai ya neme ni da aure kuma mafi yawanci bayan anyi auren da wata 2 ko 3 sai ya sake ni.”
Cikin shekara 6 na auri maza 18 kuma babu wanda muka zauna sama da wata 4 tare. Yawanci mazan suna komawa da tsana ta har ma ya kai ga bugu wasu ma abun yakai ga kokarin kashe ni.” ta furtar.
Babban faston cocin Memnen Ukum ya bayyana mata cewa satar da tayi ma gogonta lokacin da ta ziyar ce ta a Legas yayi sanadiyar ƙalubalen da take fuskanta.
Yace zata kubuta daga matsalolin da take samu indai ta mayar da abun da ta sata daga goggon.
Korchioga ta tabbatar da yin satar kuma ta aikata haka ne cikin jahilci domin sai da goggon ta biyota har inda take zaune domin amsar abun da ta dauka amma tayi mata karya cewa baya hannun ta kuma a hanyar ta komawa gida goggon ta samu hatsari inda ta mutu nan take.
Leave A Reply

Your email address will not be published.