Kotu ta daure wani magidanci da matarsa da ta kama da laifin aikata fyade ga ‘yar aikin su

0
Kotun sauraron kara dake Surulere a jihar Legas ta gurfanar da wasu ma’aurata mata da mijinta da ta kama da laifin fyade da cin mutuncin mai aikin su ‘yar shekara 10.
“Yar sandan da ta shigar da karan Anthonia Osayande ta fadawa kotun cewa mai gidan Onubogu dake da shekara 54 ya yi wa yarinyar danne yarinyar da karfin tsiya da dare a watan Afirilu sannan ita matan Gloria mai shekara 45 ta fara muzgunawa yarinyar tun daga watan Afirilu zuwa watan Satumba sanadiyyar fyaden da mijin ya yi.”
“Mai aikin ta sami rauni sanadiyyar duka da fyade da ma’auratan suka yi mata sannan kuma matan ta ki kaita asibiti.”
Ma’auratan sun ki amincewa da zargin da aka yi musu sannan alkalin kotun A. Ipaye-Nwachukwu ta bada bellin su akan Naira 400,000.
Sharudun belin da alkain ta bada ya hada da kowanen su ya kawo takardun shaidan biyan haraji wa gwamantin jihar Legas guda biyu.
Alkalin ta bada umurin kai yarinyar asibiti domin ta sami kulan da take bukata sannan ta daga sauraron karan zuwa 11 ga watan Nuwamba.
Leave A Reply

Your email address will not be published.