Dalibi ya kwankwadi madarar fiya-fiya domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarrabawa

0
 Dalibi ya sha guba domin nuna kin amincewar sa da faduwa jarraba – Ya yanke shawarar kashe kansa ne bayan da hukumar makarantar ta bayyana cewar bai tsallake daya daga cikin jarrabawar da ya sake rubutawa ba 


– Binciken ya nuna cewar yanzu haka an sallami dalibin daga asibiti Wani dalibin makarantar faltaknik dake Lafiya a jihar Nasarawa, yayi yunkurin hallaka kansa bayan da ya kwankwadi madarar fiya-fiya saboda faduwa jarrabawar daya daga cikin darussan karatun sa. 

Jaridar Punch ta rawaito cewar dalibin, Chinedu Iromuanya, ya yanke shawarar kashe kan sa ne bayan da hukumar makarantar ta bayyana cewar bai tsallake daya daga cikin jarrabawar da ya sake rubutawa ba a shekarar 2016.

Binciken jaridar ta Punch ya nuna cewar yanzu haka an sallami dalibin, dan asalin Jihar Abiya, daga asibitin Dalhatu dake garin Lafiya ranar talata, kamar yadda ma’aikaciyar asibitin da bata yadda a bayyana sunanta na ta tabbatar. 

Hakazalika hukumar ‘yansanda a jihar ta Nasarawa ta bakin kakakinta na hulda da jama’a, DSP Idrisu Kennedy, ta ce bata da labarin faruwar lamarin domin hukumar makarantar bata sanar da su ba, amma sunyi alkawarin yin bincike domin tabbatar da dalilin da yasa dalibin daukar wannan mataki. 

Leave A Reply

Your email address will not be published.