Allahu Akbar: Baturen da ya taba shirya fim din batanci kan manzo Allah SAW ya musulunta

0
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa baturen nan dan kasar Jamus da ya taba yin fim din batanci ga manzon Allah Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi wasallam a shekarun baya ya karbi musulunci. 

Shi dai wannan baturen mai suna Arnoud van Doorn kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu sun nuna cewa dan siyasa ne kuma babban jigo a wata jam’iyya mai matukar kiyayya ga musulunci ta kasar Jamus din kafin musuluntar tasa. NAIJ.com ta samu kuma cewa baturen ya kuma samu damar halartar aikin hajji jim kadan bayan da ya karbi musuluncin inda kuma ke cike da bakin ciki da nadamar zama cikin wadan da suke kiyaya ga musuluncin a da. 

Haka ma kuma dai baturen daga nan ya kuma sha alwashin sake shirya wani katafaren fim din da zai nuna muhimman kyawawan dabi’un Annabin tsira da kuma musulunci a cikin sa. Muna rokon Allah ya karbi tubar sa ya kuma sa mu cika da imani dukkan mu. Amin. 

Leave A Reply

Your email address will not be published.