Dan sanda ya harbe kansa bayan ya harbe budurwarsa

0
– Wani jami’in rundunar yan sanda ya halaka budurwarsa sannan ya kashe kansa – Abin dai ya faru ne a cikin charji ofis din rundunar da ke KwaDabeka

– Rundunar tana gudanar da sahihin bincike akan yadda lamarin ya faru Wani jami’in dan sanda ya harbe budurwarsa har lahira sannan daga bisani ya harbe kansa a cikin caji ofis din rundunar da ke birnin Durban na kasar Afirika ta Kudu. Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Kaptin Nqobile Gwale yace, jami’an wanda ke sashen binciken sirri da kawar da miyagun aiki ya fara harbe budurwarsa ne, sannan ya juyo da bindigan ya harbi kansa. 

Ita ma budurwar jami’an rundunar yan sandan ne. Mene yayi zafi: Dan sanda ya harbe kansa bayan ya harbe budurwarsa

 “Mun tabbatar da faruwar lamarin yau da safe misalin karfe 9.20, an harbe wata yar sanda yar shekara 25, sannan wanda ake zargi shima ya harbe kansa. 

“Har yanzu muna gudanar da bincike akan yadda lamarin ya faru, Ana binciken zargin kisan gila a KwaDabeka SAPS.” A yayinda yake tofa albarkacin bakinsa a kan lamarin, jami’in hulda da jama’a na SAPS, Kaptin Mazwi Mbatha yace; “wanda ake zargin kashe matar yana zaune ne a unguwar Inanda Cluster. 

Suna cikin ofis tare da Mthembu sai muka ji tana ihu, kuma tana rokon ya yafe mata.” Sannan sai mukaji karar harbin bindiga sau 4, muka garzayo zuwa ofishin amma gawar su muka tarar.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.