Ko Kunsan Illar Da Man Qara Hasken Fata Ke Haddasama Mutum Kuwa??

0

Babban Darektan da ke kula da sashen gwaje-gwajen magunguna a babbar asibitin koyarwa na Ibadan Ganiyu Arinola ya yi kira ga gwamnati da ta tsaurara dokar hana shigowa da man dake canza launin fatar jikin mutum kasarnan.
Ganiyu ya fadi haka ne da yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Ibadan.
Ya kara da cewa rashin sani da kishin bakin fata ne ya sa mutane ke amfani da man da ke canza launin fatarsu.
Ya ce amfani da irin wadadan mai na da matukar illa ga jikin mutum domin suna rage karfin garkuwan jikin mutum sannan yana kuma kawo cutar daji.
Ya ce saboda yadda man ya ke da saukin samuwa a kasuwanin kasarnan ya sa babba da yaro ke amfani da su.
Ganiyu Arinola ya yi kira ga gwamnati da gidajen jaridu da su yawaita yin tallace- tallace da zai wayar wa mutane kai game da illolin da ke tattare da amfani da wadannan mai.
Leave A Reply

Your email address will not be published.