Tana Bada ‘Yarta Mai Shekaru 12 Ayi Lalata Da Ita

0


Rudunar ‘yan Sandan jihar Cross Rivers, ta damke wata mata mai’ya’ya biyar mai Suna Mrs. Udoaka Sunday da wasu mutane uku da laifin yin lalata da ‘yarta mai shekaru goma sha biyu.


Wani makwabcinta ya fadawa jaridar Vanguard cewa matar ta kan karbi kudade daga hannun mutane masu bukatar yin lalata da yarinyar mai shekaru goma sha biyu a cikin irin wadannan mutane haeda wani tsohon Soja, mai shekaru saba’in da takwas (78) mai suna Effiom Okon.
Makwabcin nata yace daga dukkan alamu matar tana da tabin hankali, ya kara da cewa matar ta karbi Naira dubu goma sha biyar (15,000) daga hannun tsohon Sojan da kuma wasu kananan kudaden daga hannu wasu mutane uku domin suyi lalata da yarinyar.
Duk lokaci da ta dorawa yarinya talla sai ta sheda mata cewa ta bi wajan tsohon Sojan da sauran mutanen da ta karbi kudaden daga garesu, ta dai dade tana ailkata wannan aika aikan kuma akasarin wadanda mahaifiyar yarinya ke wannan harka dasu sun haura shekaru hamshi da haihuwa. Wadanda ke karban kudin fansho.

Yarinyar ce da kanta ta fadawa malaminsu a makaranta daga bisani hukumar kare yara ta gudanar da bincike abinda yay i sanadiyar kama Udoaka.
Hukumar ‘yan Sanda ta ce matar tana da ‘ya’ya biyar daga mazaje biyar kuma yanzu haka tana shayarwa.
Leave A Reply

Your email address will not be published.