Yan Biafra Sun Bar Najeriya har an kafa Gwamnatin rikon kwarya

0– Kudancin Kasar nan ta rabe ta bar Najeriya yau 
– Har an kafa Gwamnatin rikon kwarya yanzu haka 
– Daga cikin manyan ‘Yan Gwamnatin akwai Pat Utomi Wata Kungiya ta Kudancin Kasar nan ta rabe ta bar Najeriya. 

Kungiyar ta Biyafara ta nada Gwamnatin rikon kwarya yanzu haka.


Wata Kungiyar Biyafara ta BZF ta bayyana cewa ta fice daga Najeriya kuma ta nada Ministocin ta da sauran Jami’an wucen-gadi. 

Shugaban Kungiyar ta Biyafara Barista Benjamin Onwuka ya bayyana wannan a yau dinnan.

Daga cikin wadanda aka nada a Gwamnatin da za ta fara aiki gobe akwai Pat Utomi, Charles Soludo. Mary Okafor, Barth Nnaji, Amarachi Ubani. Har da wasu ‘Yan Arewa irin su Farfesa Jerry Ghana da Labaran Maku. 

Kungiyar tace Kasar Amurka na bayan ta kuma ita za ta rika sayen kayan man kasar. Kungiyar ta Biyafara tace haka kuma Kasar Israila na cikin wadanda za ta mara mata baya. 

Leave A Reply

Your email address will not be published.