Kotu ta daure wani magidanci da yayi wa ‘yar sa fyade a Minna

0
Kotu a garin Minna jihar Neja ta daure wani manomi dani shekara 20 mai suna Lawali Safiyanu domin ya yi wa ‘yar cikinsa fiyade a dakin kwanansa.
Kotu ta daure Safiyanu ne bayan sauraron karar da wani mazaunin titin Nasko da ke cikin garin Minna Dawudu Ahmadu ya shigar yana tuhumar Safiyanu da tilasta ma ‘yar cikinsa ta kwana da shi.
Lauyan da yake kare ‘yar Safiyanu Aliyu Malami ya ce Lawali ya ja ra’ayin yar tasa ce bayan ya zuga ta da ta bishi zuwa dakin sa da karfe biyu na rana wanda bayan ta shiga dakin ne ya danneta.
Aliyu ya sanar wa kotu cewa laifin Safiyanu ya saba dokar kare hakin yara na jihar Neja wanda bai kamata kotu ta bashi beli ba domin hakan zai iya hana ‘yan sanda gudanar da bincike.
Alkalin kotun Amina Musa ta yanke hukuncin daure Lawali a kurkuku sannan kuma ta daga karan zuwa 21 ga watan Agusta.
Leave A Reply

Your email address will not be published.